Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Dangane da ziyarar da sarkin na Qatar zai kawo nan Iran nan gaba kadan, shugaban kasar ta Iran din ya ce; A yayin wannan ziyarar kasashen biyu za su sake daukar matakai a fagegen ayyuka a tsakaninsu.
Shugaban kasar ta Iran ya kuma ce; Dukkanin kasashen biyu suna da azama mai karfi ta ci gaba da fadada alakar tasu.
Tun da farko dai, shugaban kasar na Iran ya taya sarkin Qatar din murnar shigowar watan azumin Ramadan mai alfarma, sannan kuma ya tabbatar da cewa; Iran a shirye take ta taimaki kasar tasa domin ganin ta gudanar da wasannin karshe na gasar cin kofin duniya na kwallon kafa cikin nasara.
342/